Adam A Zango Ya Koma Gona, Noma Tushan Arziki

Adam A Zango Ya Koma Gona

Adam A Zango Ya Koma Gona, Noma Tushan Arziki.

Shidai wannan hoto da kuke gani na jarumi Adam A Zango ya dora shi a shafinsa na Facebook inda ya rubuta cewa ya koma gona, kasantuwar noma shine tushen arziki.

Jama’a da dama sun bayyana ra’ayoyinsu kan wannan post na Facebook da shi jarumin yayi inda wasu ke ganin bai kamata a ce jarumin na zuwa gona ba, a yayin da wasu kuma suke ganin hakan yayi daidai.

Irin hakan dai ba sabon abu bane ga Jaruman Fina Finan Hausa Na Kannywood, ko a kwana kwanan ma sai da Jarumi Ali Nuhu ya wallafa wani hoto, inda hoton ke nuni da cewa jami’an tsaron ‘yan sanda Nigerian Police sun kama muggan makamai a gidan jarumi Ali Nuhu a cikin wani Film.

Wanda har wata kafar jaridar yanar Gizo Gizo ta wallafa, inda har abun ya haifar da hayani da tada jijiyar wuya tsananin Jarumin da kafar jaridar, inda daga bisani suka nemi gafararsa.

 

10 Comments

Add a Comment

Your email address will not be published.