Abida Muhammad Tace Bata Sha’awar Komawa Harkar Film

Abida Muhammad Bana Sha'awar Komawa Harkar Film

Jaruma Abida Muhammad Tace Bata Sha’awar Komawa Harkar Film.

Fitacciyar tsohuwar jarumar fina-finan Hausa ta masana’antar Kannywood Abida Muhammad ta bayyana cewa ko kadan bata sha’awar dawowa harkar shirya fina-finan Hausa kwata-kwata.

Ta qara da cewa tun da ta bar harkar ta tafi gidan mijin ta sai sana’ar ta bar bata sha’awa kwata-kwata.

Abida Muhammad wadda ta haskaka sosai a lokutan baya musamman a cikin fina-finai da dama tayi aure da dadewa inda ta zauna a dakin mijin nata har Allah yayi masa rasuwa. 

Masana harkokin fina-finai da dama dai na da ra’ayin cewa tsohuwar jarumar na daya daga cikin jaruman da Allah ya azurta da dimbin basira da ta bar gibin da kuma har yanzu ba’a cike ba a masana’antar.

One Comment

Add a Comment

Your email address will not be published.