Za’a Karama Fitattun Jaruman Fina-finan Hausa 7 A Kasar Ingila

Mujallar Fina Finai

Za’a Karama Fitattun Jaruman Fina-finan Hausa 7 A Kasar Ingila.

Labaran da muke samu ba da dadewa a nan na nuni da cewa wasu fitattun jarumai a masana’antar fina-finan Hausa da ake yi wa lakani da Kannywoood da suka tasamma akalla bakwai za su samu kyautar karramawa a kasar Ingila.

Jaruman dai kamar yadda muka samu daga majiyar mu wani babban kamfanin jarida ne na African Voice dake da hedikwatar sa a birnin Landan zai karrama zakakuran jaruman a cikin wata mai kamawa na Nuwamba kuma a ranar hudu ga wata.

Majiyarmu dai ta samu cewa wadanda jaridar zata karrama sune Nafisa Abdullahi (Jarumar da tafi fice); Hafsat Ahmed Idris (Babbar Jaruma); Halima Atete (babbar mataimakiyar Jaruma); Ramadan Booth (Babban jarumi); Sani Ahmad Yaro (Babban mataimakin jarumi); Kamal Alkali (Fitaccen mai bada umurni); Hamisu Lamido Iyantama (Fitaccen mai shirya fina finai).

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya ma dai wasu jaruman a masana’atar ta Kannywood sun amshi kyaututtuka da dama a wani buki da aka gabatar a birnin tarayya Abuja.

8 Comments

Add a Comment

Your email address will not be published.